Ba'Ameriken da ya dasa bom ya amsa laifinsa

Faisal Shahzad
Image caption Faisal Shahzad ya bayyanawa kotu cewa ba za a daina kaiwa Amurka hari ba har sai ta fice daga Iraki da Afghanistan

Ba'Ameriken nan haifafen kasar Pakistan wanda ya amsa tuhume-tuhume goman da aka yi masa da suka danganci yunkurin tayar da bama-bamai a dandalin Times Square ka iya fuskantar daurin rai-da-rai.

Faisal Shahzad ya shaidawa kotu cewa ya zabi ranar da zai kai harin ne don ta dace da lokacin da ya san dandalin Times Square a makare ya ke da mutane.

Da alkalin ya tambayi Shahzad ko ya ji wata damuwa kasancewar zai iya kashe kanan yara, ganin cewa shi ma yana da 'ya'ya biyu, sai ya ce ai Amurka ma ba ta taba damuwa idan ana kashe kananan yara a kasashen Musulmi.

Ba'Ameriken ya ce shi yana daukar kansa a matsayin sojan Musulunci ne, kuma yunkurin nasa wani martani ne ga ta'addancin da Amurka ke kaddamarwa a kan al'ummar Musulmi.

Shahzad ya tabbatar da cewa ya je kasar Pakistan don samun horo a kan yadda ake hada bam a wajen 'yan Taliban na Pakistan.

Ya kuma ce ya karbi dala dubu goma sha biyu daga wajen 'yan kungiyar ta Taliban.

Shahzad ya ce bama-bamai uku daban daban ya dasa a cikin motarsa; dukkansu kuma ba su tashi ba.

Ko da yake Shahzad ya ba da hadin kai ga masu bincike har na tsawon makwanni biyu bayan kama shi, ma'aikatar shari'a ta Amurka ta ce babu yarjejeniyar bayar da bayanai tsakaninsa da gwamnati.