An kama 'Dudus' Coke a Jamaica

Christopher 'Dudus' Coke
Image caption 'Yan sanda sun ce sun cafke Dudus ne a wani wajen binciken ababen hawa

Rundunar 'yansanda ta Jamaica ta tabbatar da cewa ta cafke Christopher Coke, wanda aka fi sani da suna Dudus, a wani wajen binciken ababen hawa a wajen babban birnin kasar, wato Kingston.

'Yan sadan dai sun yi amfani ne da wani bayanin sirri da suka samu; hakan kuma ya kai ga kame mutumin, wanda ake nema ruwa a jallo.

A watan da ya gabata ne dai mahukuntan kasar ta Jamaica suka bayar da umurnin fara farautar Dudus, bayan jinkiri na tsawon lokaci.

Wasu 'yan bindiga dadi sun killace wani yanki a Yammacin Kingston wanda aka ce yana karkashin ikon Dudus din, inda suka yi ta ba-ta-kashi da 'yansanda.

Daga bisani an sanya dokar ta-baci a yankin aka kuma tura sojoji; al’amarin da ya haifar da mutuwar mutane fiye da saba’in da uku ciki har da fararen hula da jami'an tsaro.

'Yan sandan sun ce za su so su yi tambayoyi ga mutanen da ke tare da Dudus din, wadanda suka zarga da boye mai laifi.