Majalisa ta fara tantance shugabannin INEC

Majalisar dokokin Najeriya

A Najeriya majalisar dattawan kasar ta fara tantance mutanen da shugaban kasa Dr Goodluck Jonathan ya gabatar mata da sunayensu domin nadawa shugaban hukumar zabe ta kasa da kuma kwamishinonin zabe.

A farkon watan nan ne gwamnatin ta bada sanarwar mika sunan Farfesa Attahiru Jega a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon shugaban hukumar zaben mai zaman kanta INEC, Farfesa Maurice Iwu. Hukumar zaben ta Najeriya karkashin shugabancin Parfesa Iwu ta fuskanci suka a ciki da wajen Najeriya kan gudanar da zabukan da aka rika korafin ba su cika ka'idojin zabe ba kuma suna cike da magudi.

Sai dai shugaba Jonathan ya janye sunayen wasu adaga cikin ainihin jerin sunayen daya mikawa majalisar kasa, biyo bayan korafin da wasu keyi cewa mutanen 'yan jam'iyyar PDP ne da suka tsaya takara.