Mace ta zama firayim minista a Australiya

Kevin Rudd
Image caption Kevin Rudd ya samu koma-bayan siyasa saboda karuwar shakku dangane da fa'idar shugabancinsa

A karo na farko mace ta zama firayim minister a kasar Australiya.

Matar, mai suna Julia Gillard, za ta karbi ragamar mulki ne kai tsaye bayan ta kalubalanci Kevin Rudd a shugabancin jam'iyyar su ta Labour.

Shi dai Kevin Rudd ya samu koma-bayan siyasa ne saboda karuwar shakkun da ake da shi dangane da fa'idar shugabancinsa ga jam'iyyar yayin da ake tunkarar zaben da za'a yi nan gaba cikin shekarar nan.

Saboda irin kaduwar da yayi, Kevin Rudd ya yi ta fashewa da kuka a fili yayin da ya fuskanci manema labarai a karo na karshe a matsayinsa na firayim minista.