Ana ci gaba da ceto wadanda ruwa ya hallaka a Ghana

Wuraren da ruwa yayi ma banna a Ghana
Image caption An yi asarar rayuka da dukiyoyi a wannan ambaliyar, wacce ruwan sama ya haddasa

A na nan ana ci gaba da aikin ceto a biranen Tema da Ashiama dake jihar Accra na birnin Ghana, inda akalla mutane 30 suka mutu bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliyar ruwa.

Hukumar bada agajin gaggawar kasar wato NADMO tace sama da mutane dubu uku ne suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwan.

Tun a ranar Asabar da daddare ne dai aka fara ruwan a baki dayan birnin Accra har zuwa washegari da maraice. Lamarin dai yafi kamari ne a biranen na Tema da Ashiama.

Wakilin BBC a birnin Accra Iddi Ali ya ce mutane 17 ne suka mutu a birnin Ashiama biyu a Tema daya a kauyen Dawhenya hudu a kauyen Mai Djor, sa'annan goma sha daya a garin Agona Nyakrom dake yammacin kasar.

Abin har ya kai inda sojojin ruwan kasar sukayi anfani da wasu kwale kwale na musamman don ceto mutane wadanda galibinsu suka makale a kan rufin gidajensu.

Madam Balkisu Ali wata mazauniyar Ashiama, ta shaidawa BBC cewa ambaliyar ta yi musu barna mai yawan gaske.

Tace abin har yakai ga rasa rayuka, kuma cikin wadanda suka mutu harda wata mace.

Bayanai suka ce cikin wadanda suka mutun har da wasu mutane shida da ambaliyar ruwan tayi awon gaba da wata motar bus da suke ciki a lokacin da suke kokarin ketare wani kogi.

Bude sansani

Hukuman bada agajin gaggawan dai tace ta bude wani sansani dake birnin Tema inda take tara wadanda suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwan.

Image caption Ambaliyar ta raba jama'a da dama da gidajen su

Kuma shugaban hukumar Mista Kofi Kportophy ya gayawa BBC cewa: "Mun tarasu a wani waje dake sansanin sojan ruwan kasa a birnin Tema kuma mun fara basu kayan agaji kamar abinci da barguna da katifu".

"Sai dai matsalar itace bamu da issasun kayan agajin. Muna sa ran samu karin kayayyakin don rarraba musu," in ji Mista Kportophy.

Akalla mutane sama da 3,000 ne suka rasa matsugunnansu a biranen Tema da Ashaima inda abin ya fi kamari.

Abirnin Accra ma dai an bada rahoton bacewar wasu yara biyu da wata mace guda wadanda ake kyautata zaton cewa suma sun mutu a ambaliyar ruwan.

Rahotannan dake fitowa daga yammacin kasar kuma sunce ambaliyar ruwan ta datse babban hanyan da ta hade yankin yammacin kasar da jihar Accra. Kawo yanzu ukuman bada agaji a kasar sun bayyana ambaliyar ruwan da cewa itace mafi muni a shekarun baya bayan nan a tarihin kasar. A biranen Ashiama da Tema dake jihar Accra inda ambaliyar ruwan tafi banna alkaluman da hukuman hasashen yanayin kasar ta bayar sunce adadin ruwan saman da akayi a wuraren ya kai sama da milimita 50.

Karin wahala

A halin da ake ciki kampanin tace danyen man petron kasar wato Tema Oil Refinery ya rufe wasu cikin injunan tace mansa abinda ake ganin ze iya janyo karancin albarkatun man petro a cikin kasar.

A fira da tayi da manema labarai babban jami'ar hulda da jama'a ta kampanin wato Madam Aba Lokko, tace hakan ya zama dole ne saboda bannan da ambaliyar ruwan tayi ga matatan man.

Wanda hakan ka iya jefa al'umar kasar cikin karin wahalar neman makamashi.

Hukuman bada agajin gaggawa ta kasar dai ta dora alhakin ambaliyar ruwan musamman a biranen Tema da Ashiama kan gine gine da tace wasu mazauna wuraren sukayi a magudanan ruwa.

Hukumar tace domin magance lamarin gomnati za ta ci gaba da aikin rusa dukkan gidajen da aka gina a magudanan ruwa. Tuni dai shugaban Ghana John Atta Mills ya umurci hukumomin kasar da su rusa dukan gidajen da aka gina a magudanan ruwa don kauce ma aukuwan irin ambaliyar ruwan da ta auku a wasu sassan kasar.

Shugaban kasar ya bada wannan umurni ne bayan da ya ziyarci wasu wuraren da ambaliyar ruwan tayi ma banna.