Tambari Jaku yace bai zai janye kara ba

Shugaban mulkin sijan Nijer Salou Jibo
Image caption Shugaban mulkin sijan Nijer salou Jibo

A jamhuriyar Nijar shugaban jam'iyar PNA Al'uma Alhaji Sanusi Tambari Jaku ya ce ba zai janye karar shugaban mulkin sojan kasar janar Salu Jibo da ya kai kotu ba, sai inda karfinsa ya kare.

Alhaji Sanusi Jaku ya jaddada wannan matsayin ne yayin wata ganawa da ya yi da shugaban kasar, tare da kasancewar ministan cikin gida Malam Cisse Ousman.

Ya fadi hakan ne a Yamai yayin wata hira da manema labarai.

A kwanakin baya ne dai Alhaji Sanusi Jakun ya kai karar shugaban kasar dangane da wani kuduri da shugaban ya sa hannu a kai, da ke hana duk wani dan Nijar mai shekara 70 da haihuwa tsayawa takara a zabukan da za a shirya a kasar.