Buhari ya ce ba zai karbi goron gayyar taron shugabannin arewa ba

Janar Muhammadu Buhari
Image caption Janar Muhammadu Buhari

Mutumin dake son tsayawa takarar shugaban kasa karkashin sabuwar jam'iyyar CPC a Nijeriya, Janar Muhammadu Buhari , ya yi watsi da tsarin karba karba game da shugabancin kasa.

Ya bayyana haka ne yayinda wasu 'yan arewacin Nijeriya ke gudanar da taruka domin jaddada matsayinsu na goyon bayan tsarin na karba karba.

An dai ce matakin da aka ce suna dauka domin ganin an kyale 'yan arewacin Nijeriyar tsayawa takara a zaben shugaban kasa na badi, domin karasa abin da suka kira wa'adin shugabancin arewacin Nijeriyar, bayan rasuwar marigayi shugaba 'Yar'adua.

Duk da yake an ce jam'iyyar PDP na amfani da wannan tsari, shi dai a ra'ayin Janar Buhari, yin hakan ba dimokradiya ba ne, kuma CPC ba zata goyi bayansa ba.

Sai dai wannan batu na karba - karba abu ne dake ci gaba da haddasa muhawara a Najeriya.

Masu ra'ayin amincewa da tsarin dai na ganin raba mukamai tsakanin yankuna ita ce hanyar da kawai za a bi a kaucewa wanu matsaloli na siyasa ganin irin bambance bambancen da ake su a kasar.

Yayinda kuma wadanda ba su amince da tsarin ba ke ganin wata hanya ce ta hana wa kasar samun Shugabannin da suka fi cancanta dukkuwa da cewar Jama'iyar PDP mai mulki ce keda wannan tsari.