Karanci abinci a Nijar na dada kamari

yaro na fama da yunwa
Image caption Sama da yara dubu dari hudu ne ke fama da yunwa a Nijar- inji kungiyar Save the Children.

Hukumomin bayar da agaji na kasar Burtaniya sun yi shelar neman gudunmuwar abinci ga jama'ar kasar Nijar, wadda kusan rabin al'ummar ta ke fama da yunwa sakamakon matsalar fari.

Ana gwada nauyin wani siririn yaro wanda babu lakka a jinkinshi a wani asibitin bayar da agajin gaggawa na yara 'yan kasa da shekaru biyar a kusa da Jihar Maradi a kudanci Nijar.

Abiou, wanda dan wata goma sha uku da haihuwa yana da nauyin kilo daya da rabi. Idanuwansa sun shanye, kuma kansa yafi gangar jinkisa girma.

Dakta Mourou Arouna Djimba ya ce a kusan kullum ne ake kawo kananan yara kamar Abiou asibiti, wadanda kuma ke bukatar taimakaon gaggawa.

"Bamu da isassun dakuna, a wasu lokutan mu kan sa yara biyu zuwa uku a kan gado daya. Muna da kusan marasa lafiya tamanin a dankin jinyan gaggawa, kuma da safiyar nan a karo mana yara biyar".

Saboda matsalar da Nijar din ke fuskanta, Kungiyar bayar da agaji ta Save the Children (STC) da kuma Oxfam sun kaddamar da asusun neman taimako ga al'ummar Nijar.

Kungiyar Save the Children ta ce sama da yara dubu dari hudu ne ke fuskantar barazanar mutuwa saboda yunwa a Nijar.

Image caption Yara na fama da cutar tamowa a Nijar

Matsalar yunwa a Nijar dai ta biyo bayan rashin samun damina mai albarka a kasar ne a bara hakan kuma ya yi sanidiyar karancin albarkatun gona abinda kuma ya janyo tsadar kayan abinci.

Duk da dai lokacin girbin amfanin goma ya karato, har yanzu kasar na ci gaba da fama da matsalar yunwa, a yayinda kusan mutane mliyan goma sha biyar ke bukatar taimakon abinci.

Mutane na ci gaba da layin karbar taimakon abinci a wata ci biya dake kusa da Jihar Maradi wadda itace jiha ta uku mafi girma a Jamhuriyar Nijar.

Wasu daga cikin su na ta ihu kuma suna neman tada hankalin saboda sun dade suna jira a kan layi amma basu samu abincin ba.

"An dade ba'a samu irin wannan tashin hankalin ba" Inji Khardiata Lo Ndiaye wata jami'ar Majalisar Dinkin Duniya.

"Yawaci mata ne da suka girma suke kan layi, amma saboda sun tsufa ba sa iya tsayuwa a kan layi".

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake fuskantar matsalar fari a Nijar amma dai na wannan shekarar ya fi muni. Wasu na cewa ya fi matsalar da aka fuskanta shekaru biyar da suka wuce wanda kuma ya jefa jama'ar kasar cikin wani hali.

A kauyen Makanga, wanda ke da tazarar tafiyar awa biyu daga garin Tanout, al'ummar kauyen na sayar da dabbobinsu domin siyan abinci; kuma ana ganin sana'ar kiwon dabbobi da aka fi sanin garin da ita za ta bata.

Wani dattijo a kauyen Musa Haj Haroon ya shaidawa wakilin BBC cewar dabbobinsa ne kawai ke rayar da shi kuma sun kusan karewa. "Idan na sayar da su gabaki daya ban san abin da zan yi kuma ba".

"Mutane da dama sun bar gidajen su sun fita neman abinci". Inji Ibrahim Fall, jami'in kungiyar Save the Children.

Ibrahim Fall ya ce matsalar yunwa a Nijar wata aba ce da kafafen yada labarai na duniya ba su yayata yadda yakamata ba domin jama'ar duniya su san munin matsalar.

"Muna fuskantar matsananciyar yunwa a kasar, yara na mutuwa saboda yunwa kuma ba ma samun isasshiyar gudunmuwa domin taimakawa al'umma kasar".

Shi ma dai shugaban kungiyar Oxfam a Niger Mbacke Niang ya ce: "Mun dade muna bayyanawa duniya irin matsalar dake adabar kasar amma babu wanda ya saurare mu kuma abin ya damemu matuka". Ya zuwa yanzu dai, Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta samu rabin kudin da ake bukata a Nijar domin magance matsalar yunwa a kasar.

Kuma babbar jami'a mai kula da ayyukan majalisar a Nijar a kasar Khardiata Lo Ndiaye, ta ce matsalar na kara ruruwa a kullum.