Pakistan ta yankewa Amrukawa hukunci

Pakistan
Image caption Pakistan

Wata kotu a Pakistan ta yankewa wasu Amurkawa musulmi biyar hukuncin daurin shekara goma a gidan kaso, bayan samunsu da laifin ta'addanci.

An zarge su ne da tuntubar 'yan kungiyar Al-Qaida dake Pakistan ta internate da kuma kulla kai harin ta'addanci. Sai dai mataimakin mai gabatar da karar, Rana Bakhtiar yace a wannan karar, shekara 25 ya kamata a basu, kuma alkalin ya basu shekara goma.

Shi yasa zamu daukaka kara zuwa babbar kotu. Don sake duba hukunci da kuma kara shi.

Wadanda aka yankewa hukuncin dai baki dayansu dalibai ne da shekarunsu suka kama daga 19 zuwa 25.