David Petraeus zai maye Stanley McChrystal

Janar David Petraeus
Image caption Shugaba Obama ya sanar da nadin Janar David Petraeus a matsayin kwamandan rundunonin hadin gwiwa a Afghanistan

Shugaba Obama na Amurka ya sanar da nadin Janar David Petraeus ya maye Janar Stanley McChrystal a matsayin kwamandan rundunonin hadin gwiwa na kasashen waje a Afghanistan.

Shugaban na Amurka ya sallami Janar McChrystal ne bayan ya ji ta-bakinsa dangane da wadansu maganganu da hafsan sojan ya yi a wata mujalla.

Fadar gwamnatin Amurka ta White House dai tun da farko ta sanar da gwamnatin Birtaniya shawararta ta sallamar Janar McChrystal.

Daga bisani kuma Shugaba Obama ya tattauna da Firayim Minista David Cameron, inda suka yi ittifaki a kan cewa Janar Petraeus ne ya kamata ya maye gurbin Janar McChrystal din.

Shugabannin sun kuma amince cewa kafin Janar Petraeus ya kama aiki, kwamandan dakarun Birtaniya a Afghanisatan, Laftanar Janar Nick Parker, ya jagoranci rundunonin kasashen wajen na wucin gadi.

Shugaban na Amurka ya kuma yi magana da Shugaba Hamid Karzai, wanda ya ce zai dauki dukkan matakan da suka dace don ganin sauyin ya yi nasara.

Korar Janar McChrystal dai kasada ce; to amma Shugaba Obama ya nace a kan cewa wajibi ne a dauki duk matakin da ya dace na tabbatar da ci gaba da kasancewar sojoji a karkashin ikon gwamnatin farar hula.

Nadin Janar Petraeus kuma zai kawar da hadarin da ke tattare da korar Janar McChrystal.

Shi dai Janar Petraeus shi ne maigidan Janar McChrystal kuma shi ne ya assasa dabarun yakar ta-da-kayar-baya a Iraki, wadanda kuma su ne ginshikin dabarun da Janar McChrystal ke aiwatarwa a Afghanistan.

Wannan nadin dai na bukatar amincewar Majalisar Dattawan Amurka, al'amarin da ba zai yi wuyar samu ba kasancewar 'yan jam'iyyar Republican da ke Majalisar Dokoki na kaunar Janar Petraeus.