Majalisar dattijai ta amince da Jega

Farfesa Jega
Image caption Farfesa Attahiru Jega ya sha alwashin gudanar da zabe mai inganci a kasar

Majalisar dattijan Najeriya ta amince da nadin Farfesa Attahiru Jega a matsayin sabon shugaban hukumar Zabe ta kasar.

Majalisar ta kuma amince da sauran kwamishinonin da suka bayyana a gabanta kawo yanzu.

A ranar Laraba ne dai Farfesa Attahiru Jega ya bayyana a gaban majalisar, bayan da shugaba Goodluck Jonathan ya mika sunansa domin amincewar majalisar.

Kuma ya amsa tambayoyi daga 'yan majalisar har na tsawon sa'o'i hudu.

Hakan na nufin yanzu Farfesan ne zai maye gurbin Maurice Iwu domin shugabantar hukumar zaben kasar.

Babban kalubalen dake gaban sa dai shi ne na shirya zabukan da kasar ke fuskanta a shekara mai zuwa.

A baya dai an soki zabukan da kasar ta gudanar da cewe suna cike da magudi da satar akwatuna da kuma cin hanci da rashawa.

Kuma kutuna sun soke da dama daga cikin zabukan shekara ta 2007, abisa laifin gaza bin ka'idojin da tsarin mulki ya shimfida.