Birtaniya za ta janye dakarunta daga Afghanistan

Dakarun kasashen waje a Afghanistan
Image caption Dakarun kasashen waje a Afghanistan

Firayim ministan Birtaniya, David Cameron ya ce, yana son a janye dakarun Birtaniya daga Afghanisatan cikin shekaru biyar masu zuwa.

Mr. Cameron ya ce, kodayake babu wani jadawali da za a bi kai da fata wajen janye dakarun, kamata yayi dakarun su koma gida kafin babban zaben Birtaniya da za a yi a shekarar 2015.

Ya kuma kara da cewa baya tsammanin cewar sha'anin tsaro ya inganta matuka a Afghanisatan, amma yana ganin ya zuwa lokacindakarun Afghanistan za su iya tafiyar da harkokin tsaro a kasarsu.

Birtaniya dai ita ce kasa ta biyu dake da mafi yawan dakaru a Afghanistan tare da sojoji kusan dubu goma.