Shugabannin kungiyar G8 na taro a Canada

Tambarin taron kungiyar G8 a Canada
Image caption Tambarin taron kungiyar G8 a Canada

Shugabannin kasashen dake kungiyar kasashe takwas masu karfin masana'antu na G8, sun fara tattaunawa a Canada, inda batun farfadowar tattalin arziki ke kan gaba a cikin ajandar taron.

Birtaniya ta ce, tana fatan taron zai cike gibin dake akwai game da bukatar kashe kudi don tayar da komadar tattalin arziki da Amurka ke jaddawa da kuma zaftre gibin kasafin kudin da ake hankoron yi a nahiyar Turai.

Sakataren baitulmalin Amurka Timothy Geithner dai yayi kira ga nahiyar ta turai data maida hankali kan manufofin da za su bunkasa tattalin arziki ba kawai kan zaftare kudaden da kasashen nahiyar ke kashewa ba.

A gobe ne za a soma babban taron kungiyar G20 a kasar ta Canada.