Indiya zata kara kudin Fetur

Firaministan Indiya Manmohan Singh
Image caption Firaministan Indiya Manmohan Singh

Gwamnatin kasar India tace zata kara kudin man fetur da kuma man diesel a wani bangare na rage kudaden da take kashewa na rangwamen man fetur din, ta kuma zaftare gibin kasafin kudin kasar.

Masu adawa da hakan dai na cewa matakin zai kara assasa tashin farashin kayyaki a kasar da tuni ake zanga-zangar nuna rashin amincewa shi.

Su kuwa masu goyon bayan matakin na nuni da cewa, hakan ya zama dole don karfafawa masu zuba jari a fannin makamashi kwarin guiwa.

Masu aiko da rahotannin sunce batun karin farashin man fetur nada sarkakiyar siyasa a kasar, sai dai hukuncin da gwamnatin ta dauka na kin kara kudin kalanzir zai iya saukaka bacin ran jama'a.