Amurka ta gargadi kasar Guinea Bissau

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Amurka ta ja hankalin kasar Guinea Bissau akan cinikin miyagun kwayoyi

Amurka ta gargadi gwamnatin kasar Guinea Bissau da cewa ba zata taimakawa kasar ba wajen inganta rundunar sojin ta, matukar kasar bata yi watsi da shugabannin da ake zargi sun mamaye kasuwancin miyagun kwayoyi a yankin ba.

Wata sanarwa data fito daga offishin jakadancin Amurka dake Dakar ta ce Amurka na ci gaba da mamakin yadda wasu manyan hafsoshin soji hade da fararen hula a kasar ta Guinea Bissau keda hannu dumu dumu a safarar miyagun kwayoyi.