Biritaniya za ta takaita ci-rani a kasar

Theresa May, Sakatariyar Cikin gida ta Biritaniya
Image caption An fi marhabin da kwararru

Birtaniya za ta saka kaidi daga watan gobe kan ci-ranin baki a kasar daga kasashen da ban a Tarayyar Turai ba.

Za a kyale ‘yan kwadago kusan dubu 24 daga kasashen da ba na Tarayyar Turai ba su shiga kasar daga yanzu zuwa watan Afrilun badi.

A ranar Litinin ne Sakatariyar cikin gida, Theresa May, za ta bayyana shirin.

Za ta soma tattaunawa kafin tabbatar da takaicin ci-rani kasar ga bakin da na kasashen Tarayyar Turai ba.

Daya daga cikin manyan kungiyoyin da ke daukar ma'aikata a Birtaniya ta soki kaidin, tana cewa zai haddasa karancin kwararrun ma'aikata a kasar.