Shugaba Karzai ya yi kiran yaki da miyagun kwayoyi

Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan
Image caption Noman tsirran miyagun kwayoyi ya zama ruwan dare a Afghanistan

A wannan rana ta yaki da shan miyagun kwayoyi a duniya, Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan ya ce dole ne kasashe makwabta su kara zage damtse domin hana fasa kwaurin miyagun kwayoyi irin su ofiyam a kasarsa.

Shugaba Karzai ya ce Afghanistan a karin kanta ba ta da karfin hana cinikayyar miyagun kwayoyin.

Shugaba Karzai ya jaddada kudurin gwamnatinsa na magance samar da miyagun kwayoyi a Afghanistan.

Ya ce, “Za mu yi aiki tukuru a kan noman sauran miyagun kwayoyi domin amfanin kasarmu, da daraja da kuma jin dadin rayuwar Jama'ar Afghanistan da kuma ci gaba.

Shugaba Karzai ya ce ‘yan Afghanistan sun karbi alhakin matsalar miyagun kwayoyin, to amma ya kara da cewa wasu daga waje da suka hada da kungiyoyin masu aikata manyan laifuka da kuma kasashen waje na karfafa noman kwayoyin a Afghanistan.