Kasashen G8 soki Iran da Korea ta Arewa

Taron kasashe 8 mafiya arzikkin masana'antu
Image caption Ko wane mataki suke shirin dauka a kan Iran da Korea ta Arewa?

Shugabannin kasashen nan takwas mafiya arzikin masana'antu sun yi kakkausar suka a kan kasashen Korea ta Arewa da kuma Iran.

Sun yi Allah wadai da Korea ta Arewa a kan nutsar da jirgin ruwan yakin Korea ta Kudu a watan Maris, kana suka yi kira ga shugabannin Iran da su kare hakkin bil adama, su kuma dinga aiki da doka.

Firaministan Canada, Stephen Harper, ya ce duka Korea ta Arewa da Iran sun mallaki makaman da ke barazana ga makwabtansu.

Ya ce duniya za ta dage wajen ganin kudin da suka kashe wajan sayen wadannan makamai ba shi ne kadai asarar da za su yi ba.