Shugabannin kasashen Amurka da burtaniya sun gana

Shugabannin kasashen Amurka da Burtaniya sun gana
Image caption Shugabannin kasashen Amurka da Burtaniya sun gana bayan da Firayim Ministan burtaniya ya halarci taron G8 a karon farko

Firayim Ministan Burtaniya David Cameron yayi wata tattaunawa da shugaba Obama a taron G20 wadda a karon farko ya fara halarta.

Shugabannin kasashen biyu dai sun amince da cewa dangataka ta musamman dake tsakaninsu na nan daram kamar yadda aka santa.

Sun kuma bayyana cewa dukkaninsu na daukar matakai ne na bai daya kan muhimman batutuwa da suka hada da Afghanistan da sauran batutuwan da suka shafi tattalin arziki.