Yau ake Zaben Shugaban kasa a kasar Guinea

Firimiyan kasar Guinea
Image caption Firimiyan kasar Guinea

A yau ne jama'ar kasar Guinea ke zaben shugaban kasa, bayan da kasar ta kwashe watanni goma sha takwas a karkashin mulkin soja.

'Yan takara ashirin da hudu ne dai zasu fafata a zaben wadanda suka hada da tsaffin Firayim Minstocin kasar su biyu da kuma wata mace guda.

Gabanin zaben shugaban mulkin sojan kasar, Sekouba Konate yayi alkawarin cewa a karon farko tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai fiye da shekaru hamsin, za'a gudanar da zabe na gaskiya da adalci.