Kuri'ar raba gardama a Kasar Kyrgyzstan

Kuri'ar raba gardama a Kyrgyzstan
Image caption Za'a gudanar da Kuri'ar raba gardama a Kyrgyzstan akan ko a karawa majalisun dokokin kasar karfi

A yau ne jama'ar kasar Kyrgyzstan ke kada kuri'ar raba gardama kan ko a sake karawa Majalisun dokokin kasar karfi.

Kuri'ar raba gardamar dai na zuwa ne makwanni biyu bayan barkewar wani mummunar rikicin kabilanci a kudancin kasar.

Wata Jami'a dake sa ido a daya daga cikin rumfunan da za'a kada kuri'ar a birnin Bishkek ta bayyana cewa mazauna birnin na cikin wani yanayi na doki, inda kuma zasu fito kwansu da kwarkwatarsu su kada kuri'a.