Ana kuri'ar raba-gardama a Kyrgyzstan

Wani mai jefa kuri'a a Kyrgyzstan
Image caption Gwamnati tana neman halacci

Mutanen Kyrgyzstan na kada kuri'ar raba-gardama a kan ko a rage karfin ikon shugaban kasa zuwa ga majalisar dokoki ko kuma a’a.

Gwamnatin rikon kwaryar da ta karbi iko bayan ta tilasta wa Shugaba Krmanbek Bakiyev ya sauka a watan Afrilu, ce ta shirya kuri'ar.

Shugabar rikon kwaryar, Roza Otunbayeva ta ce ana bukatar kada kuri'ar domin tabbatar da halaccin gwamnati.

Mutane na kada kuri'ar ne domin samun zaman lafiya da kuma halattacciyar Gwamnati.

A baya-bayan nan an yi mummunan artabu tsakanin al'umar Kyrgyz da kuma na kabilar Uzbek da ke zama a kudancin kasar.