Sama da yara dari na fama da tamowa a Najeriya

Sama da yara dari ne suka kamu da tamowa
Image caption Wanan yarinyar ta fara murmurewa bayan ta kamu da tamowa

Matsalar tamowa dai da ke shafuwar kananan yara a jam'huriyar Nijar sakamakon karamcin abinci ko rashin abinci mai gina ta fara shafuwar kananan yara a wasu yankuna Najeriya dake daf da jamhuriyar ta Nijar.

A makon jiya ne dai hukumomin lafiya na jahar sakkwato suka tabbatarda mutuwar yara goma sha biyu a yankin karamar hukumar Gada sakamakon matsalar ta tamowa.

Ana fargabar samun Karin kanana yaran da ke tamowar ke shafuwa a wasu yankunan jahar kamar su Ilela ,Tangaza ,Gudu da binji da kuma kamba Bunza da kangiwa a jahar kebbi.

Sai dai masana sun ce matsalar na faruwa ne saboda rashin sani daga bangaren iyaye mata na baiwa y'ay'ansu naukkan abinci mai gina jiki bawai karamcin abincinba.

Wakilinm BBC a Sakkwato Haruna Shehu Tangaza ya ziyarci Kauyen Kadadin Buda inda gidauniyar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kananan yara ta kafa wata cibiya domin farfado da yaran da suka kamu da tamowar.

Sai dai wani abun daure kai shine yadda ake samun matsalar ta tamowa a wadannan yankunan wadanda suka yi fice wajen noma a jihar.

Akan haka ne Wakilin BBC ya tambayi babban jami'in cibiyar ta Out-patient therapeutic Programme Centre da kauyen na kadadin Ahmed Muhammed Rufai ko menene yake haddasa matsalar ta tamowa a wadannan yankunan.

"Abin da ke kawo tamowa, a wadanan yankuna shine rashin sani, domin mutanen wannan yankin na noman abinci, amma rashin sanin yadda za su sarrafa shi ya zama abinci gina jiki da kuma kare jiki daga cututuka shine suka gaggara".

Image caption Abinci gina jiki da Majalisar Dinkin Duniya ta samar

Ahmed Muhammed Rufai ya ce cibiyar ta samu yara dari da sittin da hudu masu dauke da cutar a kauyukan da suke kusa da Nijar.

Sai dai wata matsalar da zata iya yin tarnakin ga kawowa yaran dauki shine kyamar zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na zamani da wasu iyayen keda amma Basarake kauyen na kadadi Alhaji Garba Muhammed Rafin Duma ya ce suna daukar matakan shawo kan wannan matsalar:

"Mun bi gida-gida kuma anyi shela, domin kira ga iyaye da su fito da yaran su saboda a bincika a tabbatar ko suna da cutar".

"Muna da bukatar isasun hanyoyi da kuma motar daukan marasa lafiya domin a riga kai yara asbibiti idan abin ya gaggare mu". In ji Alhaji Garba Mohammed Rafin Duma.

Wani abu kuma da wadannan alumomin ke bukata shine ruwan masu tsafta domin hanasu kwasar rowan sama da suka kwanta akasa domin anfani a gida kamar yadda na taradda wasu mata sunayi.