Bankunan Nijeriya har yanzu na da hadari

Wata hukuma mai auna karfin bashi mai suna Standard and Poors ta ce ta yi imani har yanzu bankunan Najeriya na cikin hadari duk da garambawul din da aka yi wa fannin bankuna a kasar.

Kakakin hukumar ya bayyana garambawul din da shugaban babban bankin kasar, Malam Sunusi Lamido Sanusi yayi a matsayin wani mataki dake nuna matukar jarunta.

Sai dai hukumar ta ce har yanzu akwai sauran rina -a -kaba.

Hukumar ta Standard and Poors dai ta sanya bankunan Najeriya a cikin sahu na biyu (B), wanda hakan ya sanya fannin bankin kasar cikin jerin fannonin bankunan da suka fi kowane hadari a duniya.