Mataimakin gwamnan Bauchi ya koma aiki

Alhaji Garba Gadi
Image caption Gwamnatin Bauchi tace za ta daukaka kara kan hukuncin kotun

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi Alhaji Muhammad Garba Gadi, wanda kotu ta mayar kan karagar mulki ya koma bakin aikin sa, cikin wani yanayi mai cike da rudu.

'Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye domin shawo kan wata hayaniyar da ta taso lokacin da Alhaji Garba Muhammad Gadi ke komawa ofishin na sa.

'Yan sandan su yi hakan ne lokacin da wasu gungun matasa suka fara 'yan kone-kone kusa da ofishin mataimakin gwamnan da safiyar yau din nan.

Hakan ya faru ne daidai lokacin da Alhaji Garba Gadi ke komawa aiki bayan da kotu ta bayar da umarnin a maida shi ofishin sa.

Majalisar dokokin jihar Bauchi ce ta tsige shi daga mukamin misalin watanni goma da suka shige.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mataimakin gwamnan ya yiwa editan mu na Abuja Ahmed Idris, bayanin cewa bin tsarin doka ne yasa shi yin gaggawar komawa bakin aikin alhali ana shirin daukaka kara kan hukuncin mai da shi.

Sannan ya kara da cewa suna fatan kotu za ta sallami majalisar jihar baki daya a hukuncin da za ta yanke a ranar biyar ga watan gobe.