A yau za'a fara zaben Burundi

Burundi
Image caption Wasu mazauna kasar Burundi

Zaben kasar Burundi

Idan an jima a yau ne al'ummar kasar Burundi za su kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar da tuni an san sakamakonsa.

Mutum daya tilo da ya rage a takarar, shi ne shugaba mai ci Pierre Nkurunziza, bayan gaba daya abokan takararsa sun janye daga zaben bisa zargin magudi a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a baya-bayan nan.

Wakilin BBC ya ce jam'iyyar da ke mulki ta bukaci masu zabe su fito kwansu da kwarkwata, su kuma yan adawa sun umarci na su da su kauracewa zaben. Kowanne bangare kuma na zargin dayan da baiwa magoya bayansa makamai don cimma manufarsa.

Wannnan ne dai zabe na farko da za'a yi a Burundi bayan yakin basasar shekaru goma sha uku.