Iran ta jinkirta tattaunawa a kan batun nukiliya

Shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad
Image caption Shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad

Shugaban Iran, Mahmoud Ahmadinejad, ya ce kasarsa za ta jinkirta sasantawa a kan shirinta na nukiliya har nan da makonni masu zuwa, domin ta hori kasashen yamma dangane da abinda ya kira: sabon takunkumin da suka sa mata.

A lokacin wani taron manema labarai a Tehran, babban birnin kasar, Mahmoud Ahmadinejad ya ce, Iran ba za ta iya komawa tattaunawar ba kamin karshen watan Agusta.

A farkon wannan watan ne kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya amince a kakaba wa Iran wani sabon takunkumin, saboda ta ki ta daina sarrafa karfen uranium.

Iran ta musanta zarge-zargen cewa tana kokari ne ta kera makaman nukiliya.