'Yansanda sun kulle ofishin mataimakin gwamnan Bauchi

Nijeriya
Image caption Nijeriya

A Nijeria 'yan sanda a jihar Bauchi sun kulle ofishin mataimakin gwamnan jihar Alhaji Garba Muhammad Gadi.

Rahotanni daga garin Bauchi dai sun ce lokacin da mataimakin gwamnan ya je ofis domin fara aiki a yau, ya tarar kofofin a kulle, sannan an girke karin jami'an yan sanda a wurin.

A makon da ya gabata ne dai, wata kotu ta bada umarni a mayar da mataimakin gwamnan kan mukaminsa, bayan da majalisar dokokin jihar ta tsige shi, kusan watanni goman da suka wuce.