Rashin wa'adi ne ya janyo matsalar karba-karba: In ji Ekwueme

Dakta Alex Ekwueme da Pat Utomi
Image caption Farfesa Pat Utomi a bangaren hagu da Dakta Alex Ekwueme a wajen taron cikar Najeriya shekaru 50 da samun 'yan cin kai a London.

Mataimakin shugaban kasa na farko a Najeriya, Dakta Alex Ekwueme ya fadawa BBC cewa matsalar da Najeriya ke fuskanta dangane da tsarin karba-karba, ta yi kamari ne saboda shugaba yana iya yin fiye da wa'adi daya na mulki.

Ya ce Babban taron da aka yi a kasar kan batun tsarin mulki a shekarun 1994 da 1995, wanda ya halarta, ya bada shawarar a kaucewa wa'adin mulki fiye da daya, amma ba'a yi aiki da shawarar ba.

Dakta Ekwueme ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taro a Landon, wanda ya tattauna irin matsalolin da Najeriya ke fuskanta tun bayan da ta samun 'yancin kai da kuma yadda za a magance su.

A hirarsu da Mohammed Jameel Yushau, wanda ya halarci bikin bude taron, Dakta Alex Ekwueme ya yi karin bayani kan ko ya kamata shugaba Goodluck Jonathan ya tsaya takara a zabe mai zuwa.

Ga yadda yadda hirar sa da BBC ta kasance.

BBC: Shin kana ganin ya kamata shugaba Goodluck ya tsaya takara a zabe mai zuwa.

Ekwueme: Ina ganin wannan tambaya ce da ba ta taso ba a halin yanzu.

Babban batun dai shi ne cewa a wancan lokaci da muka yi magana akan tsarin karba karba, ba a yi tunanin cewa shugaban kasa zai iya mutuwa ba yana kan mulki, wanda hakan zai sauya tsarin shugabancin baki daya.

Da a ce mun tsaya akan tsari na yin wa'adin mulki kwaya daya na shekara hudu ko shekara biyar, da yanzu muna kokarin wa'adin mulki ne na hudu, wato da shugaban kasa na hudu ne zai kokarin karbar mulki a shekara mai zuwa.

Image caption Najeriya kasa ce mai kabilu daban daban

BBC: To shin a ina tsarin na karba din ya samo asali ne?

Ekwueme: Batun tsarin karba-karba ya taso ne lokacin taron tsarin mulki na kasa a shekrar 1994-1995 lokacin Janar Abacha yana shugaban kasa. Ni kaina ana kirana da jagoran karba karba, saboda na yi fafutukar ganin an sami wannan tsari.

Kuma tunanin a wancan lokacin shi ne cewa ya kamata ya zamanto muna da kasa wacce kowa zai ji cewa yana da ta cewa a ciki, muna ganin hakan yana da kyau ga makomar Najeriya domin samun kwanciyar hankali da martabarta da kuma kasancewarta kasa daya.

Kuma hakikanin tunanin shi ne, idan ka duba kundin tsarin mulki na 1995 wanda muka yi, wanda kuma da Janar Abacha ya fara amfani da shi a watan Oktoba na 1998 da bai rasu ba a watan Yuni na waccan shekara, mun tsara cewa tsarin karba-karbar za a yi shi ne na tsawon shekaru talatin.

Ta hakan dukkanin yankuna guda shida na Nijeriya za su samar da shugaban kasa, kowannensu wa'adi daya na shekaru biyar. Kuma wadannan shekaru talatin za a dauke su ne a matsayin shekaru na gina kasa.

BBC: To wanne dalili ne ya sa tsarin na karba karba ya gamu da cikas?

Ekwueme: Abin takaici shi ne gwamnatin Janar Abdussalam Abubakar wacce ta karbi mulki daga Janar Abacha ba ta amince da hikimar da ta sa muka amince da wannan tsari ba a taron tsarin mulki na 1994-1995, wanda ke da nufin kafa wani tsari da zai sauya Najeriya daga kasa zuwa al'umma, wanda yana da matukar muhimmanci idan muna son mu ci gaba.

Amma kawai sai suka dauki tsarin mulki na 1979 suka yi masa 'yar kwaskwarima, saboda haka tsarin karba karba ya zama batu ne na cikin gida ga jam'iyyun siyasa.