Alex Ekwueme ya ce ba a bin tsarin karba-karba yadda ya kamata

Farfesa Pat Utomi da Alex Ekwueme
Image caption Farfesa Pat Utomi da Alex Ekwueme

Toshon mataimakin shugaban kasar Nijeria, Dr Alex Ekwueme ya bayyanawa BBC cewa matsalar da Nijeria ke fuskanta dangane da tsarin karba-karba, ta yi kamari ne saboda shugabanni na iya yin fiye da wa'adi daya a mulki.

Ya ce Babban taron da aka yi a kasar kan batun tsarin mulki a shekarun 1994 da 1995, wanda ya halarta, ya bada shawarar a kaucewa wa'adin mulki fiye da daya, amma ba a yi aiki da shawarar ba.

Dr Ekwueme yana halartar wani babban taro ne a nan London, wanda ke tattauna irin matsalolin da Nijeria ke fuskanta tun bayan da ta samu 'yancin kai da kuma yadda za a magance su.