Wata takaddama ta kunno kai a Majilisun Najeriya

Nigeria
Image caption Majilisar dokokin Najeriya

Baraka a Majilisar Dokokin Najeriya

A Najeriya a yayinda yan kasar ke jiran a kamala aiki kan kundin tsarin mulkin kasar, da aka yiwa kwaskwarima, bisa ga dukkan alamu za'a iya cewa wata takaddama tsakanin majilisar dattawa data wakilai, ka iya kawo tsaiko ga aikin, wanda yake da alaka da gyra ga dokokin zaben kasar.

Sai dai Shugaban Majilisar dattawa kasar , Senata David Mark da kuma kakakin Majilisar wakilan kasar Honarable Dimeji Bankole sukayi kace na ce dangane da wanan batu

Su dai yan majiisar wakilai sun yi zargin cewa kundin tsarin mulkin kasar, da aka mika wa Majilisun Jihohi ba shi ne wanda Majilisun biyu suka amince akai ba, ammah kuma majilisar dattawan kasar ta musanta wanan zargi

Ko da a lokacin da ake aikin gyra ga kundin tsarin mulkin dai, takaddama tayi ta kawo tsaiko tsakannin majilisar dattawa da wakilan.

A wannan lokaci dai yan majilisar sun sami rashin dai daito akan wanda zai jagoranci shugabancin kwamitin da ka dora ma alhakin yin gyra kan kundin tsarin mulkin kasar.