Yau za'a mika rahoton yin gyra ga dokar zaben Najeriya

Image caption Majalisar Dokokin Najeriya

Rahoton yin gyra ga dokar zaben Najeriya

Idan an jima ne ake sa ran cewa Majalisar Wakilan Najeriya zata karbi rahoton kwamitinta na yin gyara ga dokar zabe ta kasa, da nufin rage yawan jam'iyyun siyasar da ake dasu a kasar.

Yanzu haka dai akwai jam'iyyu hamsin da bakwai dake da ragista a Najeriya.

Wasu na korafin cewar, yawancin jam'iyyun ana kafa su ne kawai da nufin amfana da kudin tallafi da hukumar zabe ke baiwa jam'iyyun siyasa.

Koda a baya dai anyi kokarin kayyade yawan jam'iyyun siyasar da za'a yiwa rajista a Najeriya, amma wasu masu rajin dimukradiyya sun kalubalanci wannan mataki.