Majilisar Najeriya zata gana da jamian sojin kasar

Nigeria
Image caption Majilisar dokokin Najeriya

Majilisa Najeriya zata gana da shugabannin sojin kasar

A yau ake sa ran kwamitin kula da harkokin tsaron majilisar wakilan Najeriya, zai yi wani zama da manyan hafsoshin rundunonin sojin kasar, dangane da korafe korafen da suka biyo bayan shirin yiwa wasu jami'an soji saba'ain da tara retiya.

Su dai wadanda ake shirin yiwa retiya sun yi zargin cewa, ana kokari ne kawai a raba su da aikinsu, a dai dai lokacin da suke shirin samun karin girma

Wadanda lamarin ya shafa, sun hada da masu mukamin kyaftin da kuma birgediya janarar.

Honarable Auwalu Abdu Gwalabe memba a kwamiti ya fada wa BBC, cewa mnaufar zaman ita ce su tabatar cewa hukomomin sojin kasar sun bi kaida a matakin da suka dauka.