Janar Petraeus kan yaki a Afghanistan

Janar David Petraeus a gaban majalisar dokokin Amurka
Image caption sabon kwamandan dakarun kawance a Afghanistan, Janar David Petraeus.

Mutumin da shugaba Barack Obama ya zaba domin jagorantar sojojin kawance a Afghanistan, Janar David Petraeus ya yi gargadin cewa fadan da ake yi a kasar ta Afghanistan tsakanin sojojin kawancen da mayakan Taliban zai iya kazancewa a 'yan watanni masu zuwa.

Ya kuma yi alkawarin kara daukar matakan da suka dace na murkushe masu tada kayar baya a Afghanistan din.

Janar Petraeus yana bayani ne a gaban wani kwamitin majalisar Dattawan Amurka, wanda zai tabbatar da shi a mukaminsa don maye gurbin Janar Stanley McChrystal, wanda shugaba Obama ya kora a makon jiya.