Kotu ta ce ana iya karar Pfizer a Amurka

A Najeriya, kungiyar iyayen yaran da gwajin maganin kamfanin Pfizer ya shafa a jihar Kano ta bayyana jin dadinta da shawarar da Kotun kolin Amurka ta yanke na tsame hannunta daga takaddamar da ke tsakaninsu da kamfanin.

Yau ne dai Kotun Kolin ta yi watsi da karar da kamfanin na Pfizer ya daukaka, yana kalubalantar hukuncin da wata kotun daukaka kara ta yanke cewa za a iya sauraron koken iyayen yaran a kotunan kasar Amurka.

Su dai iyayen yaran sun shigar da kara ne a Amurka, suna zargin kamfanin na Pfizer da keta dokokin kasa-da-kasa da suka haramta yin gwajin magani a kan mutane ba da izininsu ba.