Talauci a wasu jihohin Najeriya

Matsalar karancin abinci kasar Nijar ta shafi Najeriya
Matsalar karancin abincin da ake fama da ita a Niger ta sa wasu mutane a wasu jihohin Najeriya da ke makwabtaka da Nijar din sun fara fuskantar matsalolin rayuwa.
A jhar katsina dake makwabtaka da Nijar, rohotannni na cewa an samu yawaitar 'yan karkara dake shigowa birni saboda karancin abinci.
Ga alama yunwar ce sakamakon rashin kudin sayen abinci ta sa, a yanzu haka tsofaffi ke tururuwa zuwa birane a Katsina suna yawon bara.
A kwanakin baya ne gwamnatin Najeriya ta aikewa Nijar tallafin hatsi ton dubu goma sha biyar, kana ta saki ton dubu biyar, don a saidawa talakawan Najeriyar akan farashi mai rahusa.