Taliban sun kara da dakarun NATO .

Sansanin da 'yan Taliban suka kai wa farmaki a Afghanistan.
Image caption Hare hare a Afghanistan dai na ci gaba kusan a kullum.

Dakarun kungiyar tsaron NATO sun ce, sun fatattaki mayakan Taliban, wadanda suka kai wani babban hari a babban sansaninsu da ke gabashin Afghanistan. A cewar NATOn, 'yan Taliban din sun kai harin ne da bindigogi da kuma rokoki, a sansanin jiragen saman da ke wajen birnin Jalalabad.

Rahotanni na cewa an kashe da dama daga cikin maharan.

Jiya Talata, mutumin da shugaba Obama ya zaba a matsayin sabon kwamandan sojan Amurka a Afghanistan, watau Janar David Petraeus, ya ce akwai yiwuwar tashin hankali zai karu a can, a watanni masu zuwa.