Farfesa Jega ya yi rantsuwar kama aiki

Attahiru Jega
Image caption Sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, Attahiru Jega

Yau da rana ne aka rantsar da sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, INEC, Parfesa Attahiru Jega, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

An rantsar da shi ne tare da kwamishinoninsa da kuma sakatarorin hukumar zaben.

Rantsarwar ta biyo bayan tantance shi, tare da kwamishinonin na tarayya da majalisar dattawan kasar ta yi a makon da ya wuce.

A baya dai hukumar zaben Nijeriyar ta sha suka kan shirya zabe maras inganci, mai cike da magudi a kasar.

Wasu dai na yi wa kallon nadin sabon shugaban hukumar zaben, a matsayin wata alama ta kyautatuwar al'amurran zabe a Nijeriyar.