An yi wata hatsaniya a unguwar Ijora ta Legas

Yansandan Najeriya
Image caption Yansandan Najeriya

A Najeriya rundunar 'yan sandan Jihar Legas ta tsaurara matakan tsaro a unguwar Ijora, bayan wani tashin hankali da ya haifar da kone-kone.

Wasu rahotanni na cewa mutane da dama sun jikkata, a rikicin da ake wa ganin ya faru ne tsakanin sassan da ba sa ga maciji da juna.

Babu dai bayanin ko suwa suka haddasa wannan al'amari.

Amma dai Yansanda sun samu shawo kan rikicin.

Kuma yanzu haka suna sintiri a yankin domin kara bayar da kwarin guiwa ga mazaunansa.