Gwamnonin arewacin Najeriya na taro a Kaduna

Taswirar Najeriya

A Najeriya, a yau ne gwamnonin arewacin kasar ke taron yini guda don tattaunawa kan al'amurran da suka shafi yankin, wanda shi ne karo na farko tun bayan rasuwar shugaba Umaru Musa 'Yar'adua.

Ana sa ran gwamnonin za su karbi rahoto wucin gadi kan farfado da kamfanin buga jaridu na New Nigeria da kuma wani rahoto game da garonbawul ga kamfanin NNDC.

Haka kuma gwamnonin na sa ran ganawa da tawagar shugabannin kungiyar 'yan siyasan arewa da kuma wani kwamiti da zai shirya wani taron siyasa na arewacin kasar.

Sai dai taron na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ma'aikatan kamfanin buga jaridun na New Nigeria ke korafi game da matsalolin da kamfanin ke ciki da shakkunsu game da aniyar gwamnonin na farfado da kamfanin.