Kungiyar NATO ta ce ba zata sauya manufofinta a Afghanistan ba

Janar David petreaus
Image caption Sabon kwamandan dakarun kungiyar NATO a Afghanistan.

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta ce nadin sabon kwamandan sojojin kungiyar a Afghanistan, ba ya nufin za'a kawo sauyi a manufar kungiyar.

Sakatare-Janar na kungiyar, Anders Fogh Rasmussen, ya ce ba za'a sauya manufar kungiyar ba na murkushe 'yan Taliban da kuma baiwa sojojin Afghanistan damar tafiyar da harkokin tsaron kasarsu.

Ya kuma ce Janar Petraeus, wanda ya bayyana a gaban jami'an kungiyar a birnin Brussels don yi musu bayani kan sabon mukaminsa, na da goyon bayan kungiyar ta NATO dari bisa dari.

Janar David Petraeus ya bayyana cewa kungiyar Taliban ta kara samun nasarori a farkon wannan shekara, amma ya ce a kwanan baya, kungiyar taliban ta yi asarar mayakan ta da dama.