Somalia ta cika shekaru 50 da 'yancin kai

Shugaban Somaliya, shaikh Ahmad
Image caption Shugaban Somaliya ya gargadi 'yan kasar su gyara kurakuarnsu ko kasar ta watse

A yau ne Somaliya, wadda ake ganin tana cikin kasashen da suka fi koma-baya a duniya, ke cika shekaru hamsin da samun mulkin kai.

A ranar daya ga watan Yuli na shekarar dubu da dari tara da sittin ne dai yankin kudancin kasar da ke karkashin mulkin Italiya ya hade da arewacin kasar wanda ya samu mulkin kai daga Burtaniya kwanaki biyar kafin nan.

A halin da ake ciki yanzu dai gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, tana iko ne da wani bangare na babban birnin kasar, Mogadishu kawai.

Sai dai yayin da ake shirye-shiryen bukukuwan murnar cikar kasar ta Somaliya shekaru hamsin da samun mulkin kai, ita kuwa kungiyar bayar da gaji ta Red Cross hankalinta ne ya tashi sakamakon harba wata roka da aka yi a kan wani asibitin da ta ke kula da shi a arewacin Mogadishu.

Rokar dai ta lalata wani gini inda majinyata ke zaune suna jiran ganin likita, ta kuma hallaka majinyaci daya, ta kuma yiwa wani rauni.

A cewar kungiyar ta Red Cross, halin da ake ciki a kasar ya kai intaha tun da hatta a asibiti ma mutane ba su kubuta ba.

Wannan harin dai ya tabbatar da abin da shugaban kasar ta Somaliya ya fada ranar jajibirin bukukuwan samun mulkin kan.

A cewarsa, ya rage wa 'yan kasar ta Somaliya su gyara kurakuran da suka tafka a baya ko kuma kasar ta narke.

Tashe-tashen hankula na kusan shekaru 20 dai sun mayar da mutanen Somaliya miliyan uku marasa galihu wadanda suka dogara a kan agajin da suke samu daga kasashen wajen.