Amurka ta dakatar da agaji ga Afghanistan

Kakakin Majalisar Wakilan Amurka, Nancy Pelosi
Image caption Majalisar Wakilan Amurka ta ce ba za a ba Afghanisatn agaji ba sai an binciki hanyoyin da ta sarrafa kudaden da aka ba ta a baya

Kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilai ta Amurka ya dakatar da bayar da agaji ga kasar Afghanistan har sai majalisar ta binciki zargin jami'an gwamnatin Afghanistan din da ake yi da laifin karkatar da kudaden da ya kamata a yi ayyukan raya kasa da su zuwa wasu bankuna a kasashen waje.

Kwamitin dai ya amince da kashe fiye da dala biliyan hamsin da shida a kan harkar diflomasiyya da bayar da agaji ga kasashen waje.

Amma ya dakatar da shirin na aikewa da agajin na kusan dala biliyan hudu zuwa Afghanistan.

Shugabar kwamitin, Nita Lowery ta ce tana goyon bayan aiwatar da ayyukan da aka shirya kashe kudaden a kansu, wadanda suka hada da ilmantar da mata da kula da lafiya da kuma tallafawa kananan manoma.

Sai dai a cewarta, ita da abokan aikinta sun damu matuka da wani rahoto da jaridar Washington Post ta wallafa wanda ya yi zargin cewa antoni janar na kasar ta Afghanistan na fuskantar matsin lamba daga gwamnati a kan ya dakatar da binciken wasu mutane da ake zargi da laifin cin hanci da rashawa.

Rahoton ya kuma zayyana yadda ake sulalewa da damin kudi ta babban filin sauka da tashin jiragen sama na Kabul zuwa kasashen ketare.

A yanzu haka dai antoni janar na Amurka, Eric Holder, na Afghanistan din don ganewa idanunsa irin kokarin da ake yi na kawar da cin hanci da rashawa da kuma safarar miyagun kwayoyi.

Kwamitin ya ce ba zai amince a ba Afghanistan kudin ba har sai an binciki hanyoyin da kasar ta bi wajen sarrafa kudaden agajin da Amurka ta ba ta a shekaru ukun da suka gabata.