Shugaba Obama na son gyaran dokar shigi da fici

Shugaba Barack Obama
Image caption Ko yana shirin gabatar da sabuwar doka ne?

Shugaba Obama ya yi kiran da a yiwa manufar shigi da ficen Amirka gagarumin garambawul, yana mai cewa tsarin da ake da shi yanzu ya sukurkuce, kuma yana tattare da hadari.

A jawabinsa na farko da ya yi kan batun a matsayinsa na shugaban kasa, Mr Obama ya ce ya yi imanin cewa Amirkawa za su iya mantawa da bambance-bambancen ra'ayin dake tsakaninsu, don bullo da wani tsari da zai yi aiki.

Ya ce, “Hanya daya da za mu tabbatar cewa yunkurin da muke yi na gyara al'ammura bai sake yin rauni ba saboda banbancin ra'ayin siyasa, ita ce 'yan siyasa na duka jami'yu biyu su kudiri anniyar warware wannan matsala ga baki dayan ta.

Mr Obama ya kara da cewa matakin yiwa bakin hauren dake Amirka ahuwa ko kuma na tesa keyarsu kasashensu, ba hanya ba ce da ta dace don tinkarar matsalar ta bakin haure su kusan miliyan 11 dake zaune a Amirka.