Za a yafewa Congo basussukan da ta ci

Taswirar kasar Congo
Image caption Akasarin al'ummar Congo na fama da matsanancin talauci

Bankin Duniya da Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) sun amince da wani shiri na shafe bashin da ke kan Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.

A hukumance, kasar Congo ta cancanci shiga shirin yafewa kasashe matalauta na Asusun IMF da kuma Bankin Duniya, matakin da zai kai ga sokewa kasar bashin kusan dala biliyan takwas, wato kashi casa'in na bashin da ake binta.

Shugaba Joseph Kabila ya so a kammala cimma matsaya a kan shirin yafiyar kafin bukukuwan cikar kasar shekaru hamsin da samun mulkin kai, to amma kasar Canada ta bukaci a yi jinkiri saboda dalilan shugabanci da kuma hakkin hakar ma'adanai.

Masu nazari a kan al'amura dai sun ce soke bashin ba zai inganta rayuwar talakawan kasar Congon ba, ko da yake zai inganta kimarta a idon masu zuba jari na kasashen waje.

Bayan shekara da shekaru ana fama da rikice-rikice da kuma koma-bayan tattalin arziki, mutanen Congo da dama na rayuwa ne cikin matsanancin talauci.

Idan da mahukuntan kasar ta Congo za su yi abin da ya dace, to wannan wata dama ce ta samar da hanyoyin tunbuke talauci a kasar.