David Petraeus ya isa Afghanistan

David Petraeus
Image caption David Petraeus

Sabon kwamandan sojojin kawance dake Afghanistan Janar din sojan Amirka, David Petraeus ya isa kasar ta Afghanistan, 'yan sa'o'i bayan da wasu 'yan kunar bakin wake suka afka wa ginin wata kungiyar bada agaji ta Amirka a birnin Kunduz na Arewacin kasar.

Wakilin BBC ya ce Janar Petraeus ya isa kasar ta Afghanistan ne a lokacin da wasu ke nuna shakku a game da cigaban da sojojin kawance ke cewa suna samu a kasar inda 'yan kunar bakin wake ke kai hare-hare 3 a kowanne sati.

Duka 'yan kunar bakin waken da suka kai harin na Kunduz dai sun mutu a lokacin musayar wutar da suka yi da masu gadin wurin, kuma an kashe akalla wasu karin mutanen 4, ciki har da baki 3 ma'aikatan agaji.