An kashe mutane ashirin da daya a Mexico

Taswirar kasar Mexico
Image caption Kungiyoyin sun jima suna fafutukar karbe iko da yankin kan iyakar kasar da Amurka

Jami'an gwamnatin Mexico sun ce an kashe akalla mutane ashirin da daya a wata karawa da aka yi tsakanin wadansu kungiyoyi biyu na masu safarar miyagun kwayoyi a kusa da kan iyakar Mexicon da Amurka.

Tuni dai an kama mutane tara, kuma hukumomin lardin na Jihar Sonora da ke arewacin kasar sun ce kungiyoyin biyu da suka kara sun yin fice wajen yin fasa kwaurin miyagun kwayoyi da ma mutane zuwa Amurka.

Kungiyoyin biyu dai sun jima suna fafutukar karbe iko da yanki na kan iyaka.

Dubban mutane sun rasa rayukansu a tashe-tashen hankulan da ke da alaka da fataucin miyagun kwayoyi a Mexico a 'yan shekarun da suka gabata.