Mutane 37 sun mutu a harin bom a Pakistan

Harin kunar bakin wake a Pakistan
Image caption Hare-haren bom dai ba bakon abu bane a Pakistan, amma an dade ba a kai harin kunar bakin wake ba

'Yan sanda a Pakistan sun ce wasu 'yan kunar bakin wake biyu sun kai hari kan wani wurin ziyara na addini a gari na biyu mafi girma a kasar, inda mutane akalla talatin da bakwai suka mutu, wasu fiye da dari da saba'in kuma suka yi raunuka.

'Yan kunar bakin waken sun kai harin ne da maraicen jiya Alhamis a daidai lokacin da wurin ziyarar a garin Lahore ke makare da dubban mutane.

Jami'an tsaro a Pakistan sun dade sana zargin masu kishin Islama da laifin kai hare-hare a wurare daban daban a kasar.

Dan kunar bakin wake na farko dai, a cewar jami'an 'yansanda, ya tashi bama-baman da ke jinkinsa ne a wani babban dakin karkashin kasa inda maziyarta a wurin ziyarar da ake kira Data Darbar ke kwanciya.

Ya kuma tashi bama-baman ne a daidai lokacin da ake rabawa maziyartan abinci.

Shi kuwa dan kunar bakin wake na biyu ya tashi nasa bama-baman ne a wata farfajiya da ke kofar shiga wurin yayin da mutane ke rububin gujewa hari na farko.

Wannan harin dai ya auku ne a daidai lokacin da dubban mabiya wani waliyyi ke ziyara a wurin, inda nan ne kabarinsa.

Daya daga cikin wadanda suka yi rauni, Mian Aamir, ya ce da yawa daga cikin mutanen da suke tare da shi sun mutu:

Image caption Daya daga cikin 'yan kunar bakin waken ya tashi bama-baman da ke jikinsa ne a farfajiyar wurin ziyarar

“Na ji sautin fashewar wani abu mai tsananin kara, a lokacin ina zaune; kuma akasarin mutanen da ke zaune tare da ni sun mutu.

“Akwai kuma kusan mutane ashirin da ke salla; babu daya daga cikinsu da ya rayu”.

Garin Lahore dai, wanda ke da muhimmanci ta fuskar siyasa da aikin soji da ma al'adu, ya sha fama da hare-hare masu muni a shekara gudan da ta gabata.

Wannan harin ya kuma zo ne a daidai lokacin da jami'an 'yansanda ke yiwa juna barka ganin cewa a karo na farko a shekara guda ba a kai harin kunar bakin wake a kasar ba.

An dade dai ana fama da hare-hare daga masu tada kayar baya a kasar ta Pakistan, wadanda ake alakantawa da kungiyar El-qaeda, wacce aka yi amannar tana da karfi sosai a kasar ta Pakistan.

Har yanzu dai ba a san wanene ke da lahakin kai harin ba.