ECOWAS na babban taro a Cape Verde

Tambarin kungiyar ECOWAS
Image caption Shugabannin kasashen ECOWAS na kokarin bunkasa masana'antu

Shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, wato ECOWAS, suna wani babban taro a tsibirin Cape Verde da nufin samar da wata manufa ta bai-daya ta bunkasa masana'antu.

A wata sanarwa, kungiyar ta ECOWAS ta ce taron zai amince da wata manufa ta bunkasa masana'antu da ake fatan za ta karfafa matsayin kasashen kungiyar nan da shekarar 2030.

Shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, yana halarta taron shugabannin kasashen ECOWAS din a wani bangare na ziyarar da yake yi a wasu kasashen Afirka da suka hada da Equatorial Guinea, da Kenya, da Tanzania, da Zambia da kuma Afirka ta Kudu.

Kasar Brazil dai na so ne ta fadada hada-hadar kasuwancin da ke tsakaninta da kasashen Afirka.