Joe Biden ya kai ziyara Iraki

Joe Biden
Image caption Joe Biden

Mataimakin shugaban Amruka, Joe Biden yana Iraki don nuna goyon baya ga shugabannin kasar, wadanda ke kokarin kafa wata sabuwar gwamnatin hadin gambiza.

Sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin Irakin da aka yi a cikin watan Maris, wanda bai ba wani bangare rinjaye gaba gadi ba, ya sa harkokin siyasa sun kara dagulewa a kaar.

Mr Biden zai gana da shugabannin manyan jam'iyyun siyasar kasar ta Iraki, don karfafa musu gwiwa su gaggauta tattaunawar da suke yi kan batun kafa sabuwar gwamnati.

Amruka dai tana da niyyar janye ragowar sojojinta dake Irakin nan da karshen watan Agusta.